| 07.01.2009 | 17:00 UTC
Halin da ake ciki a Gaza
Bayan tsagaita wutar sa´o´i ukku , Isra´ila ta koma yin ɓarin wutar da ta fara yau da kwanaki 12 a zirin Gaza.
Saidai duk da da cigaban da wannan hare -haren hukumomin Isra´ila, sun yi na´am da tayin shiga tsakanin da Masar tayi domin cimma tsagaita wuta kamar yadda ministar harakokin waje Zipi Livni ta bayyana:
"Bamu da matsalar zama domin tattanawa, da zaran tattanawar zata cimma tudun dafawa, to kuma za mu cigaba da tsagaita wuta sa´o´i ukku ko wace rana."
Itama Ƙungiyar Hamas tace a shirye take ta hau tebrin shawara da shugaba Hosni Mubarack a game da batun.
Sadai kamin nan, a ƙasashe dabam dabam na duniya, a na cigaba da zanga- zangar nuna adawa ga wannan hare- hare.
bayan zanga zangar da ta wakana a ƙasashen larabawa da wasu ƙasashen turai, a kwanaki baya, yau a Jamhuriya Niger , Tarayya Nigeria, Senegal da Mali, dubunan masu zanga zanga sun shirya tafiyar jerin gwano cikin lumana, domin la´antar hukumomin bani yahudu.
Rikicin iskan Gaz
Ƙasar Russia ta gitta sharadin aika masu sa ido ga batutun Gaz na ƙasar Ukraine, wanda ke jigilar iskan Gaz ɗin da take sayarwa ƙasashen Turai, kafin ta buɗe yawan addadin wannan makamashi.
Tsakanin jiya da yau, kamfanin Gazprom ,ya rage matuƙa gayya yawan Gaz ɗin da yake shayar da Ƙasashen turai a dalili da rikicin da ya ɓarke tsakanin Russia da Ukraine.
Ƙasashen Turai da dama wanda suka haɗa da Hongrie, Bulgaria, Austraiya, Jamhuriya, Tcheque da sauran su ,sun shiga zullumin fuskantar matsalar Gaz.
Shugaban hukumar zartaswa na Ƙungiyar Tarayya Turai, Jose Manuel Barosso, yayi kira ga ƙasashen biyu, sun himmantu ,domin kawo ƙarshen wannan taƙƙadama.
Gobe alhamis za a tattanawa tsakanin kamfanin Gazprom na Russia da takwaransa Natftogaz na Ukraine a birnin Brasssels, sda zumar lalubo hanyoyin cimma yarjejeniya.
Idan dai ba a manta ba ,ranar 1 ga watan da muke ciki Russia ta kaste batutuwan gaz da take sayarwa Ukraine, a dalili da rashin jituwar da ta haɗa ƙasashen biyu a game da farashe da kuma bassusuka.
Hare-hare a Afghanistan
A ƙasar Afghanistan, ana cigaba da kare jini biri jini, tsakanin dakarun ƙasa da ƙasa da ´yan taliban.
Sanarwar daga rundunar tsaro ta NATO ta bayyana kashe mayaƙanTaliban 50 tsakanin jiya da yau ,a yankin Laghman dake matsayin ɗaya daga manyan sansanonin Taliban.
To saidai har ya zuwa wannan lokaci, babu sanarwa daga ɓangaren Taliban da ta musanta kokuma gaskanta labarin.
Sojojin Ƙungiyar tsaro ta Nato tare da haɗin gwiwar dakarun gwamnati sun ɗauri aniyar fatatakar ´yan taliban a wannan shekara.
Don cimma wannan buri, Amurika ta yanke shawara ƙara yawan sojojinta.
Tun bayan kifar da mulkin Mollah Umar, a shekara 2001 ake fafatawa tsakanin sojojin ƙasa da ƙasa, da ´yanTaliban, ba tare da NATO ta cimma burin kawo ƙarshen wannan Ƙungiya ba, da Amurika da ƙasashenTurai ,suka jera sahun Ƙungiyoyin ´yan ta´ada.
An rantsar da saban shugaban ƙasar Ghana
Bayan ´yan Majalisun dokoki, babban kotin ƙolin ƙasar Ghana ta rantsara da saban shugaban ƙasa Pr John Atta Mills, gaban dubun- dubunan jama´a a birnin Accra.
A yayin da ya karɓar rantsuwar Pr Atta Mills yayi rantsuwa da zai gudanar da mulki kamar yadda dokokin ƙasa suka tanada.
Jim kaɗan bayan rantsuwa yayiwa ´yan majalisar Dokoki jawabi, inda yake cewa:
"Kamar yadda na bayyana, ni shugaba ne na dukkan ´yan Ghana wanda suka zaɓe ni da wanda ba su zaɓe ni ba,yanzu lokacin zaɓe ya kau, babu batun NDC Ghaan kokuma NPP Ghana, sai kawai batun al´ummar ƙasar Ghana mai ɗauke da buri ɗaya, na cigaban ƙasa."
Shima mataimakin shugaban ƙasa wato, John Dramani Mahaman, yayi rantsuwa da gudanar da aiki daidai yadda dokokin suka yi tanadi.
Anyi wannan biki, tare da halartar shugaba mai barin gado, John Kuffor, da kuma shugabanin Afrika da dama da suka haɗa da Tarayya Nigeria, Jamhuriya Benin, Liberia, Siera Leone, Togo Senegal da Burkina Faso.
John Atta Mills zai jagorancin ƙasar Ghana, a tasawn shekaru huɗu masu zuwa, ya kuma alƙawarta yin aiki tuƙuru don haɓɓaka tattalin arziki da kyautatta rayuwar al´umma.







