| 01.12.2008 | 19:00 UTC
Indiya ta gabatar ƙorafi ga Pakistan
Ƙasar Indiya ta yi kiran jakadan Pakistan domin gabatar masa da ƙorafi a game da harin taáddanci da aka kai a birnin Mumbai. Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu na neman yin tsami sakamakon alakar yan takifen da ƙasar Pakistan. Jamián bincike na ƙasar Indiya sun ce yan takifen da suka kai wannan harin da ya hallaka mutane kusan 180 dukkanin su yan asalin Pakistan ne. A waje guda kuma jamaá na ƙara fusata bisa rahotanni dake baiyana cewa gwamnatin ta yi burus da kashedin da aka yi mata game da yunƙurin yan takifen na kai hari. Tuni wannan badaƙalar ta sanya masu manyan jamián gwamnatin waɗanda suka haɗa da Ministan cikin gida da gwamna da kuma ɗan majalisar dokoki na jihar Maharashtra suka yi murabus.







