| 01.12.2008 | 19:00 UTC
Yarjejeniyar cinikayya
Manyan jamián cinikayya daga ƙasashen Brazil dana tarayyar Turai sun baiyana kyakyawan fatan samun nasara a tattaunawar Doha kan yarjejeniyar cinikayya. Tarayyar turai da kuma Brazil sune akan gaba wajen matsa ƙaimi don kammala tattaunawar cinikayyar wadda aka shafe kusan shekaru bakwai ana muhawara akai. Suka ce hakan zai taimaka wajen ƙara angizo don ceto taɓarɓarewar tattalin arziki da ake fama da shi. Ministan harkokin wajen Brazil Celso Amorim a hira da manema labarai ta haɗin gwiwa da ya gudanar tare da kwamishiniyar cinikayya ta ƙungiyar EU Catherine Ashton yace yana da ƙarfin gwiwar zaá cimma matsaya kafin ƙarshen wannan shekarar. Sabuwar yarjejeniyar da ake fatan amincewa da ita zata rage rangwamen haraji da kuɗin fito akan kayayyaki masu yawa waɗanda ake safarar su zuwa ƙasashen ƙetare.







