| 01.12.2008 | 19:00 UTC
Taron Muhalli a Poland
Shugabanin siyasa da masana kimiyya sun ja hankali da cewa matsalar da ake da ita ta hada hadar kuɗaɗe na iya wucewa amma matsalar ɗumamar yanayi abu ne da ka iya zama na dundundun matuƙar ƙasashe basu haɗa kai wajen shawo kan hayaƙin masanaántu dake gurɓata yanayin ba. Da yake jawabi ga wakilai fiye da dubu goma da suka halarci taron, shugaban hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da kare yanayin muhalli Yvo Boer yace lokaci na neman ƙurewa na shawo kan wannan matsala. Wakilai daga ƙasashe kusan 190 ke halartar taron na makwanni biyu wanda ke da nufin samar da sabuwar yarjejeniya da zata maye gurbin yarjejeniyar Kyoto ta shekarar 1997 wadda ta buƙaci wasu ƙasashe su rage hayaƙin masanaántun da suke fitarwa da kashi biyar cikin ɗari kafin nan da shekara ta 2012.







