Duniyar ɗan Adam | 27.11.2008
EU ta ɓullo da tsarin yaƙi da talauci
null
A cigaba da luluben hanyoyin magance matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma durƙushewar bankuna, da duniya ke fuskanta Ƙungiyar Tarayya Turai ta ɓullo da wani sabairi.
Yammancin jiya ne ƙasashen Ƙungiyar Tarayya Turai su 27 suka kamalla zaman taro a birnin Brussels, inda suka tattana a game da hanyoyin da ya cencenta su bi, domin kawo ƙarshen matsalar tatallain arziki da rugurgujewar bankuna , kamfanoni da masana´antu da dake shirin zama gagarabadau.
Sanarwar ƙarshen taro tace Ƙungiyar Tarayya Turai ,zata ware zunzurutun kuɗi Euro miliyan dubu dari biyu a matsayin tallafi ga bankuna kamfanoni da masana´atu.
Wannan kuɗi ya kai mizanin kashi 1, 5 kawai na albarkatun cikin gida da ƙashen EU su ka mallaka ako wace shekara.
A yayin da yake jawabi a ƙarshen shugaban hukumar zartaswa ta Ƙungiyar tarayya Turai Jose Manuel Barosso , ya bayyana mahimmanci ɗaukar wannan ƙwaƙƙwaran mataki.
"A halin dake ciki mun shiga wani mummunan yanayi na taɓarɓarewar tattalin arziki, amma a sakamakon wannan tsari, ko shakka babu za mu tada komar tattalin arzkinmu, kuma EU za ta fusknaci wannan ƙalubale na musamman."
Ranekun11 da 12 ga weata mai kamawa shugabanin ƙasashen EU za su shirya zaman taro na mussamman inda za su yanke shawara a game da fasalin.
Idan ya samu tabaraki, tun farkon shekara ta 2009 zai fara aiki, kuma tallafi zai cigaba har zuwa shekara ta 2010.
Daga jimlar kuɗaɗen, ƙasashen EU 27 ko wace zata bada gundumuwa, ta yadda zasu tattara a ƙalla Euro miliyan dubu 170, to saidai ba a tantance yawan kason da ko wace ƙasa za ta badawa ba.
Sauran giɓin Euro miliyan dubu 30 za su fito daga assusun Tarayya na birnin Brussels, da kuma babbar bankin ƙasashen turai.
Tunni wannan kasafi na ƙungiyar Tarayya Turai ya fara samun suka daga masana harakokin tattalin arziki, wanda ke ɗaukar sa a matsayinn "ba a rabi da bukar ba".
Sannan kamin daukar matakin bai daya a fadar mulkin birnin Brussels tuni wawsu manyan ƙasashe Turai wanda suka haɗa da Jamus, France da Engla sun ɗauki matakan cikin gida.
A wani ɓangaren ayar tambaya da masana harakokin tattalin arziki ke yi, itace ta ƙaƙa ƙasashen sabin shiga a Ƙungiyar EU zasu yi kwaskwarima kai tsaye ga baitilmaninsu, domin biyan kuɗaɗen na karo -karo ,mussamman idan aka dubi matsalolin da suke fama da su.
Jose Manuel Barosso ya maida masu martani tare da cewa:
" Idan ba yanzu ba, to sai yaushe ne ƙasashen EU za su gama ƙarfi su gudanar da kwaskwarima ga asusunansu ?"
Domin ƙara tallafawa wannan tsari, Ƙungiyar tarayya Turai tayi kira ga membobinta suka kara yawan kuɗaɗen zaman kashe wando da suke tallafawa marasa aikin yi, wanda a halin yanzu, ke cikin halin tsaka mai wuya, ta la´akari da hauhawar farashen kaya, sannan gwamnatocin EU, su ƙara yawan tallafi ga iyalai masu ƙaramin albashi ta hanyar rage masu haraji.














